HUKUMAR KAROTA TA GARGADI JAMI’ANTA A KAN KARBAR NA GORO DAGA HANNUN DIREBOBI

Hukumar kula da harkokin zirga zirgar ababen hawa ta jihar Kano wato KAROTA ta gargadi Jami’anta su guji tunkarar masu ababen hawa a yayin da suke tsaka da gudu akan tituna.
Hukumar tace matakin ya ci karo da dokokin da suka shata ayyukan ta.
A zantawa da gidan Radio Dala Fm, wasu direbobin mota sun koka tare da nuna damuwa game da yadda jami’an hukumar ta KAROTA ke tunkarar su a yayin da suke tsaka da gudu akan tituna.
Haka zalika, direbobin sunyi korafin cewa, jami’an na hukumar KAROTA na kokarin karbar na goro a hannun su, duk kuwa da cewa, sun bi ka’ida wajen daukar fasinjoji.
A martaninta ga wannan korafi, hukumar ta KAROTA tace wannan dabi’a da wasu jami’an ta ke nunawa ya yin gudanar da ayyukan su, ba ta bisa ka’aidar aiki, kuma babban hadari ga lafiyar jami’an da kuma direbobi da kuma fasinjojin mota.
Malam Murtala Salisu Abdullahi dake zaman kakakin hukumar ta KAROTA yace duk jami’in da suka kama da irin wannan dabi’a babu shakka zasu dauki hukunci mai tsanani akansa.
A don haka nema, kakakin hukumar ta KAROTA ya shawarci direbobi su kai rahotan duk wani Jami’in hukumar daya nuna wannan dabi’a ko kuma ya nemi na goro a hannun sa.
COV KI/MIK

en_USEnglish
en_USEnglish