KOTUN KASUWAR KURMI TA FARA SAURARON SHARI’AR ABINCIN DABBOBI

Babbar kotun Shari’ar Musulunci mai zamanta a kasuwar kurmi karkashin alkali Faruk Ahmad ta fara sauraron wata kara da wani mutum mai suna Sa’idu Muhammad ya shigar yana karar Auwalu Muhammad bisa zargin cewa dabbobin Auwalun sun cinye masa harawar dankali da rake na kimanin naira dubu 70
sai dai lauyan wanda ake kara ya musanta da’awar, kotun tayi umarnin ya kawo shaida.
Alkalin kotun ya sanya ranar 16 ga wannan watan don cigaba da shari’ar.

en_USEnglish
en_USEnglish