YAN NAJERIYA SUNYI MARTANI GA YUNKURIN GWAMNATI NA RABA KUDADEN DA AKA KARBO DAGA KASAR SWITZERLAND

A makon jiya ne gwamnatin tarayya ta sanar cewa, hukumomin kasar Switzerland sun dawo da Karin dala miliyan 322 daga cikin kudaden da akace shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha ya boye a can.
Dangane da haka ne gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin rarraba wadannan kudade ga wasu ‘yan najeriya dake fama da talauci su dubu dari uku da biyu wadanda suka fito a 19 daga cikin jihohin kasar nan 36.
Tuni dai gwamnatin tarayyar ta ayyana fara raba naira dubu biyar-biyar ga wadannan mabukata daga cikin wannan kudi, farawa daga wannan wata na Yuli.
Akan haka ne gidan Radio Dala ya jiyo ta bakin wasu ‘yan najeriya a nan Kano wadanda suka bayyana mabanbantan ra’ayi.
“yayin da wasu ke ganin matakin ya dace, wasu kuwa na cewa ba ta wannan hanyar ya kamata gwamnati ta kashe kudaden ba, suna masu ra’ayin cewa kamata yayi gwamnati tayi amfani da kudaden wajen samar da ayyukan raya kasa, kamar asibitoci, titinan mota, makarantu, da raya ayyukan noma.”

Rahotanni sun nuna cewa, nan da makwanni kalilan masu zuwa ne gwamnatin tarayya zata fara aikin rarraba kudaden da akace shugaba Abacha ya boye a kasar Switzerland dala miliyan 322 ga matalauta a kasar nan.
MIK

en_USEnglish
en_USEnglish