GWAMNATIN JIHAR EBONYI TA HARAMTA SIYAR DA MAGUNGUNAN TRAMOL DA CODIEN.

Gwamnatin jihar Ebonyi ta haramta siyar da magungunan tramadol da Codeine a dukannin shagunan siyar da magani dake fadin jihar.
Mai taimakawa gwamna a harkokin lafiya, Dakta Sunday Nwangele, ne ya sanar da hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Abakaliki.
Ya ce haramta siyar da magungunan zai fara aiki ne nan take sai dai kawai illa likita ne kadai ya rubuta maganin.
Ya kumace magungunan sukan gusar da hankali ne kawai yayin da matasa ke sha ba bisa ka’ida ba wanda kuma hakan kan lalata kwakwalwa.
Ya kara da cewar,gwamnatin jihar na sane da irin matasan da suke ta’ammali da irin wadannan magungunan wanda kuma laifi ne shan su.

en_USEnglish
en_USEnglish