RUNDUNAR YAN SANDAN SARS SUN CAFKE MUTANE 37.

Sashin dakile aiyukan fashi da makami na rundunar ‘yansanda wato SARS, sun cafke wasu mutane 37 da ake zargin su dauke da addina a garin Ukelle dake karamar hukumar Yalla a jihar Cross River.
Kwamandan sashin, Mista Victor James Usang ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai jiya Talata.
Ya ce, matasan an kama su ne a kan iyakar jihar Cross River da Ebonyi a cikin mota kira bus tare da wasu matasa.
Ya kuma ce, sun sami nasarar kama matasan ne, bayan sanar da su da wani matashi ya yi ta hanyar tarho kuma basu yi kasa a gwiwa ba suka kama su.
Ya kara da cewar, tuni suka tantance matasan wanda suka gano cewa sun fito ne daga garin Uyo na jihar Anambra, wadanda kuma za suje wajan tsuma kan su a wani waje da ake kira Oju a jihar Benue.

en_USEnglish
en_USEnglish