SHUGABAN KASAR FARANSA YA SHAWARCI MATASAN NAJERIYA

Shugaban kasar Faransa, Emanuel Macron, ya shawarci matasan Nijeriya da su tsunduma harkokin siyasa a dama dasu domin kawo sauyi a harkokin siyasar kasar nan.
Emanuel Macron, yayi wannan kiran ne yayin ziyarar da yakai jihar Legas, inda ya ce,matasan Nigeria za su iya sauya fasalin kasar matukar zasu shigo a dama da su a harkokin siyasa.
Ya kara da cewa, idan akayi lakari da abin da yake faruwa a nahiyar Afrika ayanzu, matasa nada muhimmiyar rawar takawa acikin harkokin siyasar, kasar nan, a don haka ya zama wajibi ga matasa su shiga harkokin siyasa.
Emanual macron ya kuma ce, siyasa nada matukar muhimmanci don haka kamata yayi kowa ya shiga adama da shi.

en_USEnglish
en_USEnglish