HUKUMAR BADA AGAJIN GAGGAWA TA JIHAR KANO TA GARGADI KANANAN HUKUMONIN GABASAWA DA GEZAWA.

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano ta gargadi Shugabannin kananan hukumonin Gabasawa da Gezawa da sauran mazaunayankin da suyi shirin kotakwana game da hassashen da masana sukayi na Samun ambaliyar ruwa a Wannan Shekarar.
Sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano wato SEMA Aliyu Bashir Nukel, ya bayyana hakan yayin ziyarar wayar da Kai game da ambaliyar ruwa da yakai kananan hukumonin Gabasawa da Gezawa da ake zargin ambaliyar zatafi karfi a nan Kano.
Aliyu Bashir Nukel, ya kuma ce akwai bukatar shugabannin Kananan hukumonin Biyu su tattara Dagatai da Masu Unguwanni Don daukar Matakin da ya kamata Wajen Kare ambaliyar.

A nasa jawabin Shugaban karamar hukumar Gabasawa Alhaji Mahe Garba Garun Danga, yace zasuyi amfani da shawarwari da hukumar ta basu Don Kare rayuka da Dukiyar alummar yankin da ake zargin lamarin zai fi shafa.

Shi kuwa Shugaban karamar hukumar Gezawa Hudu Usman Zainawa, cewa Yayi karamar hukumar Gezawa Na bakin kokarinta Wajen rage ambaliyar ruwan sai dai Suna Fama da zaizayar kasa a wasu bangarori Dan haka akwai bukatar dauki Daga gwamnati jiha.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa hukumar bada agajin gaggawar ta jihar Kano na jahankalin sauran kananan hukumonin su tabbatar sun Yashe magudanan ruwansu tare da kaucewa yin gini a hanyar ruwa.

en_USEnglish
en_USEnglish