WANI SABON RAHOTAN KUNGIYAR KARE HAKKIN BIL’ADAMA YA ZARGI JAMI’AN TSARON HABASHA DA AIKATA FYADE DA AZABTARWA KAN FURSUNONIN SIYASA A GIDAN YARIN

Wani sabon rahotan kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch (HRW) ya zargi jami’an tsaron Habasha da aikata fyade da azabtarwa kan fursunonin siyasa a gidan yarin jihar Somali da ke gabashin kasar.
Kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta tattara shaidunta ne a tattaunawar da ta yi da mutum sama da 100 da aka tsare a gidan yarin na Ogaden tsakanin shekarar 2011-2018.
Maria Burnett ta kungiyar ta ce, rahotan na dauke da cikakkun bayanai kan cin zarafin da aka aikata a tsawon shekaru kan fursunoni.
Ta kuma bayyana yadda ake musu tsirara da lakada musu dukan tsiya a gaban sauran mutanen da ake tsare dasu.
Matan kuma da suma ke tsare, sun bayyana yadda suke haihuwa a gidan yari sakamakon fyade da masu gadin fursunan suke yi musu.
Rahotan na HRW ya kuma ce akasarin fursunonin mutane ne da ke jiran ayi musu shari’a.

en_USEnglish
en_USEnglish