A WATAN DISAMBAR BANA NE SABON JIRGIN SAMA MALLAKAR NAJERIYA ZAI FARA AIKI

Ma’aikatar kula da harakokin sufurin jiragen sama a kasar nan, ta ce daga nan zuwa karshen wannan shekara ake fatan sabon kamfanin jirgin saman najeriya zai fara aiki.

Ministan ma’aikatar Hadi Sirika ne ya bayyana hakan, yayin da yake karbar takardar shedar amincewa da yarjejeniyar kasuwanci daga babban jami’in hukumar kula da mika ragamar tafiyar da kadarorin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (ICRC), injiniya Chidi Izuwah.

Ya ce, zuwa watan Disambar bana ake sa ran kamfanin jiragen saman na Najeriya zai fara aiki.

Sanata Hadi Sirika yayi bayanin cewa, kamfanin jirgin saman na hadin gwiwa ne da ‘yan kasuwa, yana mai cewa, matakin shine ma fi dacewa, kuma za’a dauki lokaci mai tsawo ana cin moriyarsa.

Ministan ya kuma musanta ikirarin da wasu ke yi cewa farfado da kamfanin jiragen saman na kasa zai durkusar da kamfanonin jiragen sama na ‘yan kasuwa dake aiki a kasar.

A hannu guda kuma wasu na ganin farfado da kamfanin jirgin sama na Najeriya zai taimaka wajen samun saukin tsadar farashin tikitin shiga jiragen sama na ‘yan kasuwa a Najeriya.

Ko da yake kamfanonin jiragen saman na cewa dole kujerar jirginsu ta yi tsada saboda yawan kudaden harajin da suke biyan gwamnati.

en_USEnglish
en_USEnglish