APC RESHEN JIHAR KWARA BA ZA TA TABA JUYA WA BUKOLA SARAKI BAYA BA

Jam’iyyar APC reshen jihar Kwara ta ce ba za ta taba juya wa shugaban majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki baya ba.

Shugaban jam’iyyar Ishola Fulani ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda yana mai nanata cikakken goyon bayan su ga sanata Saraki.

Mr Ishola Fulani a cikin sanarwar ya kara da cewa, shugabancin jam’iyyar APC a Kwara zai ci gaba da biyayya ga shugaban majalisar dattawan.

Kalaman shugaban APC na jihar Kwara na zuwa ne kasa da mako guda da kotun koli ta wanke Sanata Saraki daga tuhumarsa da aka yi masa game da yinkarya wajen bayyana kadarorinsa, kamar yadda dokokin kasa sukayi tanadi.

Gwamnatin tarayya ta jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta gurfanar da sanata Bukola Saraki a gaban kotun da’ar ma’aikata tun a shekara ta 2015.

en_USEnglish
en_USEnglish