IYAYE A GWALE SUN KOKA GAME DA RASHIN GURBIN KARATUN ‘YAYAN SU A ISLAMIYYA

Iyaye a yankin kananan hukumomin Gwale da Kumbotso a nan Kano sun koka bisa rashin samun guraben da zasu sanya yayansu a Makarantar Tarbiyatul Aulad Chiranci Yamma, dake Chiranci a Karamar hukumar Kumbotso a nan Kano.

Wasu cikin Iyayen sun bayana cewar sun ziyarci harabar Makarantar tun da sanyin safiyar Asabar da ta gabata kamar yadda hukumar Makarantar ta shelanta don samarwa yayansu gurbi a Makarantar.

Sun kuma kara da cewar hukumar Makarantar ta kuma dakatar da sayar da takardar daukar daliban ne batare da mafi yawan su samu ba.

Sai dai Shugaban Makarantar ta Tarbiyatul Aulad Chiranci Yamma, Malam Mahadi Abdulmuminu Sulaiman, Cewa yayi suna bakin kokarinsu wajen daukar daliban amma karancin ajujuwa ne ya tilasta musu takaita daukar daliban.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa Iyaye da sauran mazauna yankin na fatan hukumar da gwamnati zasu rubanya kokarinsu wajen Inganta Iimi Musamman na Addinin Musulinci.

en_USEnglish
en_USEnglish