JAKADAN NAJERIYA A SAUDIYYA YA MUSANTA ZARGIN CEWA YANADA HANNU AKAN BATUN SAFARAR MATA ZUWA KASA MAI TSARKI

Jakadan Najeriya a Saudiyya Isa Dodo ya nesanta kansa da zargin cewa yana da hannu wajen kai mata da sauran mutane Saudiyya don aiyukan hidima inda su kan kare cikin wahala da nadama.

Jakadan na maida martani ne ga rahotan wata jaridari dandalin yanar gizo mai lakabin SECRET REPORTERS ta wallafa, inda rahotan ya alakanta jakadan da wannan lamari da ya yi kama da fataucin bil adama.

Alhaji Isa Dodo ya ce kullum shi da jami’an sa na kara kaimi don bin kadun ‘yan Najeriya da su ka samu matsala.

A Kwanakin da suka shude an samu mata mazauna Saudiyya da ke kokawa kan jefa su cikin ukuba da a ke yi a Saudiyya.

Wasu kungiyoyin Islama da aka zarga da hannu a wannan jigila sun yi watsi da zargin da hakan ya sanya kamfanonin kai mutane Saudiyya su ka fito karara su ka ce su ke wannan aiki kuma suna da rejista da duk hukumomin da su ka dace.

en_USEnglish
en_USEnglish