KUNGIYAR KWADAGO TA KASA NLC TA RUFE OFISHIN KAMFANIN MTN A KANO

Kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano ta rufe ofishin kamfanin sadarwa na MTN saboda abin da kungiyar ta kira tauye hakkokin ma’aikatan kamfanin.

Da sanyin safiyar litinin din nan ce, kungiyar ta yi biyayya ga umarnin uwar kungiyar ta kasa wadda ke umartarr assan ta na fadin kasa su dauki wannan mataki domin tilastawa mahukuntan kamfanin na MTN suyi abinda ya kamata game da walwalar ma’aikatansa.

Kungiyar dai na zargin kamfaninna MTN da laifin hana ma’aikatansa kafawa ko kuma shiga kungiyoyin kwadago a kasar nan.

Shugaban kungiyar ta NLC na kasa reshen jihar Kano Comrade Kabiru Ado Minjibir yayi karin haske ga manema labarai game da wannan mataki.

Yace baya ga kamfanin MTN, kungiyar ta NLC zata dauki makaman cin wannan mataki a kan sauran kamfanonin sadarwa na kasar nan dake haramta wa ma’aikatan su shiga ko kuma kafa kungiyoyi da nufin gwagwarmayar kwato ‘yanci.

Babban Jami’i mai kula da ofishin kamfanin MTN na Kano Abdulhamid Hassan yace “tuni suka baiwa ma’aikatan su damar shiga kungiyoyi, yan amaicewa, kamfanin na kokari ainun wajen sauke hakkokin ma’aikata da ke rataye a wuyansa.”

Wakilinmu Auwal Rabiu Fanisau ya ruwaito cewa, a yayin gangamin rufe ofishin na MTN a nan Kano shugaban kungiyar ta NLC na tare da sauran jagororin kungiyar a nan jihar Kano.

en_USEnglish
en_USEnglish