HUKUMAR KIYAYE HADURA TA KASA TA YI GARGADI GAME DA GUDUN TSERE SA’A

Hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar kano ta gargadi masu ababen hawa da su kaucewa gudun wuce sa’a yayin da suke kusanto mahadar titi, don rage yawan afkuwar hadura da kanyi sanadiyar asarar dukiya dama rayukan al’umma.

 Kakakin Hukumar Kabiru Ibrahim Daura ne ya bayyana hakan yayin zantawa da gidan rediyon Dala.

Ya kara da cewa “ya zama wajibi masu ababen hawa su ke yiwa junansu uzuri a lokacin da suke tuki.”

 Wakilin mu Abba Isa Muhammad ya ruwaito cewa, “ko da a ranar juma’ar da ta gabata, wani hadari na mota ya wakana wadda yayi sanadiyar jikkata mutane da dama a mahadar Titin hauren shanu, sakamakon shigowar wani mai mota da ake zargin ya fito ne daga lokon zai hau titi.”

en_USEnglish
en_USEnglish