SAKATAREN MAJALISAR DINKIN DUNIYA DA SHUGABAN GUDANARWAR KUNGIYAR KASASHEN AFRIKA SUN BUKACI HADIN KAN HUKUMOMIN BIYU DOMIN SHAWO KA TASHIN HANKALIN DA AKE SAMU A AFRIKA

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban gunadarwar Kungiyar Kasashen Afrika Musa Faki Muhammad, sun bukaci hadin kan hukumomin biyu domin shawo kan tashe-tashen hankulan da ake samu a nahiyar Afrika.

A wani taro da suka saba gudanarwa duk shekara, shugabannin biyu sun mayar da hankali kan yadda za a rika magance rikice-rikicen da ake samu ta hanyar nazarin abin da ke haddasa su da kuma karfafa matakan siyasa da mutunta bangaren shari’a.

Taren ya kuma duba kalubalen tsaro da zaman lafiyar da ake fuskanta a kasashen Burundi, da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Yankin Chadi da Cmaru da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, da Madagascar da Mali da Somali da kuma Sudan ta Kudu, in da shugabannin suka amince su kara yawan goyan bayan da suke bayarwa domin tabbatar da zaman lafiya.

Shugaban Kungiyar Kasashen na Afrika, ya yi wa Guterres bayani kan matsayin taron shugabannin Afrika da aka gudanar a baya-bayan nan, yayin da kuma ya ba shi karin haske kan rikicin yammacin Sahara da na kasar Libya da kuma farfado da gidauniyar zaman lafiya ta kasashen Afrika.

en_USEnglish
en_USEnglish