WANI MASANIN HALAYYAR DAN ADAM DAKE KWALEJIN ILIMI A NAN KANO YA BAYYANA SON ABIN DUNIYA A MATSAYIN ABIN DA KE TAYA TABARBAREWAR HARKAR KOYARWA A KASAR NAN

Wani Masanin Halayyar Dan Adam dake kwalejin Ilimi ta Tarayya a nan Kano Dakta Yunusa Kadiri ya bayyana son abin duniya a matsayin abin da ke taka rawa wajen tabarbarewar harkar koyarawa a kasar nan.

Dakta Yunusa Kadiri ya bayyana hakan ne yayin tattaaunarwa da wakilin mu Buhari Isah a ofishin sa a jiya litinin.

Ya ce, “kwadayi ne ya rufewa al’umma idanu a yanzu, a don haka mafi yawancin mutane a wannan lokacin basa son har kar koyarwa.”

Dr Yunusa Kadiri ya kara da cewa, “sai Gwamnati ta mutunta koyarwa sannan al’umma za su dauketa da muhimmanci.”

Dr Yunusa Kadiri ya kuma ja hankalin matasa da su rungumi harakar koyarwa don tallafawa harkar ilimi a kasar nan.

en_USEnglish
en_USEnglish