OFISHIN JAKADANCIN AMURKA A NAJERIYA YA BUKACI GWAMNONIN JIHOHIN KASAR NAN SU KARFAFA MATAKAN TSARO A FADIN KASAR

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya bukaci gwamnonin jihohin kasar nan da su karfafa matakan tsaro musamman jami’an ‘yan sanda wajen basu horo da kayan aiki domin samar da ingantaccen tsaro a fadin kasar nan.
Hakan ya fitone ta bakin Mataimakin shugaban ofishin jakadancin Amurka a Nigeria David Young, a yayin wata ziyara da yakai jihar Plateau, don jajantawa al’ummar jihar akan rikicin da ya faru a Barikin Ladi.
A yayin ziyarar tasa David Young, ya nuna takaicinsa ga irin barnar da rikicin ya haifar, inda ya kira ga gwamnati da ta dauki matakan kawo karshen tashe tashen hankali a kasar nan.
Mr. David Young ya ce ya kai ziyarar ne domin ya fahimci abun dake faruwa, ta yadda za’a hada karfi da karfe wajen hana sake aukuwar lamarin anan gaba. Ya ce “kamata yayi a taimakawa wadanda rikicin ya rutsa dasu, tare da samar da sabbin tsaren tsaren tabbatar da zaman lafiya a yankin.”
Mr Young ya kara da cewa “yakamata Nigeria ta tashi tsaye wajen aiwatar da doka, ta hanyar samar da ‘yan sanda da horas dasu tare da basu kayan aiki da kuma albashin su, domin su gudanar da ayyukansu na tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu.”

en_USEnglish
en_USEnglish