AL’UMMAR ‘YAN KUSA DAKE KARAMAR HUKUMAR KUMBOTSO SUN YI KIRA GA GWAMNATIN JIHA DA TA SAMAR MASU DA RANDAR WUTA WATO TRANSFOMER

Al’ummar garin ‘Yan Kusa dake karamar hukumar Kumbotso dake nan Kano, sun yi kira ga gwamnati da ta samar masu da randar wuta wato Transformer don tsamo su daga halin duhu sakamakon karancin wutar lantarki a yankin.
Mazauna yankin sun yi wani gangami ne a safiyar yau juma’a a kofar gidan dagacin na Yan Kusa inda suka bayana cewar rashin hasken lantarkin abu ne da ya dade yana cimusu tuwo a kwarya.
Sun kuma kara da cewar sun yi duk iya kokarin su wajen sanar da mahukunta game da halin da suke ciki amma shiru har zuwa yanzu.
Da yake jawabi dagacin na Yan Kusa wanda wakilin sa Mustapha Isah,yayi magana a madadinsa cewa a matsayinsu na iyayen kasa Suna bakin kokarinsu wajen share hawayen mazauna yankin na yan kusa.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa mazauna yankin na kuma kokawa game da karancin ruwan sha da magudananan ruwa wanda suke fatan gwamnati zata sharemusu hawayensu.

en_USEnglish
en_USEnglish