HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA SHIRYA DAN DAUKAR BAYANAN KWAKWKWAFI GA MANIYATA.

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, ta ce daukan bayanan kwakkwafin kowane maniyacci a na’ura mai kwakwalwa da aka fara da maniyatan shiyar karamar hukumar Dala, sabon tsarine da hukumar Saudiyya ta fito da shi a bana wanda ya zama wajibi a kan dukan maniyacci.
Shugaban hukumar Muhammad Abba Dambatta ne, ya bayyana hakan a ganawara sa da gidan Rediyon Dala a safiyar yau.
Ya ce, hukumomin Nijeriya da sauran kasashe sun yi kokarin ganin hukumar ta saudiyya ta dage sabon tsarin zuwa shekara mai zuwa duba da cewar, ya zo a kuraren lokaci amma hakan ya faskara, a don haka ne hukumar ke jan hankalin maniyyata da su yi hanzarin gaggawar amsa kira daukar bayanan a duk lokacin da aka kirawo su.

Ya kuma ce matukar ba a dauki wadannan bayanai ba, hukumar ta Saudiyya ba za ta amince da shigar sa kasar ba.

A yayin da alhazan kasar Nijeriya za su fara tashi a ranar 21 ga wannan watan da maniyyatan jihar Kogi, a nan jihar Kano kimanin kujeru kasa da dubu 3 aka siyar daga cikin adadin kujeru dubu 5500 da aka warewa jihar.

en_USEnglish
en_USEnglish