BARISTA YAKUBU ABDULLAHI DODO YAYI KIRA GA GWAMNATI DA TAYI AMFANI DA DOKA WAJEN AIWATARWA DA AL’UMMA AYYUKAN RAYA KASA

Wani Lauya mai zaman kansa anan Kano Barista Yakubu Abdullahi Dodo, yayi kira ga gwamnati da tayi anfani da doka wajen aiwatarwa da al’umma ayyukan raya kasa.
Barista Dodo yayi wannan kiran ne ta cikin shirin Shari’a a aikace na nan gidan rediyon Dala da safiyar yau.
Ya ce, “matukar gwamnati zata yi la’akari da doka to babu shakka za ta gudanar da ayyukan raya kasa ga al’umma.”

Ya kara da cewa “alumma nada damar su sauya gwamnati ko wacce iri ce idan har batayi musu abinda ya dace ba, musamman ma a lokacin zabe, ko su fito su bayyana albarkacin bakinsu matukar bai saba da doka ba ga gwamnati.”

Barista dodo ya kuma ja hankalin alumma dasu kasance masu biyayya ga gwamnati maimakon aibata ko zagin gwamnati.

en_USEnglish
en_USEnglish