GWAMNAN JIHAR BENUE YA FICE DAGA JAM’IYYAR APC

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya sanar da fitar sa daga jam’iyar APC.
A yayin bikin rantsar da sabon mashawarcin sa na musamman a kan harkokin kanana hukumomin jihar a yau Litinin, gwamnan yace tuni jam’iyar APC ta kore shi.
Sai dai, gwamnan Ortom, bai bayyana jam’iyyar daya koma ba.
Amma yace nan bada jimawa ba, zai baiyanawa al’ummar jihar makomar sa.
Samuel Ortom, ya kuma yi kira ga al’ummar jihar cewa, da su zama tsintsiya madaurinki daya, yana mai cewa, lallai ya kamata su guji duk wani al’amari ya raba kawunnan su.

en_USEnglish
en_USEnglish