HUKUMAR KWASTAM TA YI KIRA DA AL’UMMA SU GUJI SIYAN MOTOCI MARASA CIKAKKUN TAKARDU

Hukumar kwastam ta yi kira da al’umma su guji sayan motoci marasa cikakkun takardu.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar mai kula da shiyar Kano da Jigawa Isa Danbaba ya yi kiran yayin zantawa da wakilin Radio Dala FM.

Ya ce sayan mota mai takardu na gaske shi ne zai fitar da mutane daga kangin fargaba da gudun fadawa hannun dakarun hukumar kwastam.
Kakain hukumar ta kwastam a nan Kano ya kara da cewa, “ko a makon daya gabata jami’an hukumar sun kai sumame wasu wuraren da ake sayar da motoci a nan kano kuma sunyi awon gaba wasu motocin da ake zargin ba su da cikakkun takardun.”

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa hukumar ta kwastam ta bayyana cewa duk motar da jami’anta suka kama a wajan da ake sayar da motocin muddin tana da takardun da ake bukata, babu shakka za’a mayarwa mai ita.

en_USEnglish
en_USEnglish