KUNGIYAR ‘NAJERIYA MAZAUNA KASAR AFRIKA TA KUDU NA NUNA DAMUWA GAME DA KISAN WANI DAN NAJERIYA DA KE ZAUNE A CAN

Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta kudu ta nuna damuwa, game da kisan da ‘yan bindiga suka yi wa wani dan kasar nan da ke zaune a can.

Shugaban kungiyar, Adetola Olubola wanda ya tabbatar da haka ga kamfanin dillancin labarai na kasa game da faruwar al’amarin, yace wasu ‘yan bindiga ne suka kashe Martin Ebuzoeme a birnin Johannesburg a ranar 12 ga watan Yulin da muke ciki.

Adetola yace “anyi kisan ne kwana daya bayan shugaban kasar Afrika na kudun Cyril Ramaphosa, ya kawo wata ziyarar aiki nan Najeriya.”

A yayin ziyarar, shugaban na Afrika ta kudu yace “galibin masu yin kisan suna ikirarin rashin aikin yi da yayi yawa tsakanin matasan kasar.”

Babban jami’i a ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Johannesburg Godwin Adama, yace “babu abinda ya hada wannan kisan da harin kin jinin baki,” inda yace “yankin da aka yi kisan ya yi kaurin suna wajen aikata miyagun ayyuka.”

en_USEnglish
en_USEnglish