MAJALISAR DATTAWA SUN NUNA ADAWA KAN DOKAR KAFA YAN SANDAN JIHOHI

Majalisar Dattawa sun nuna adawa kan dokar da za ta baiwa Jihohi izinin kafa rundunar ‘yansanda karkashin ikon gwamnatin jiha.
Dokar da take neman akafa rundunar ‘yansandan jiha ta sami karatun farko agaban majalisar dattijai sabanin abin da ya faru da dokar a baya.
Sai dai wasu daga cikin ‘yan majalisar ciki har da shugaban masu rinjaye sanata Ahmad Lawal, inda ya ce akwai bukatar a kara nazari sosai akan dokar.
Sanata Lawal ya kara da cewa akwai bukatar a gano menene ya ke hana hukumomin tsaro hana aukuwar tashe-tashen hankula.
Shima Sanata Kabiru Garba Marafa bai goyi bayan kafa rundunar ‘yansanda karkashin ikon jihohi ba, inda ya ke kira ga ‘yan arewa da suyi Magana da wakilan su a majalinsun tarayya da kakkausar murya na nuna adawar su da wannan kudiri.
Kakakin majalisar dattijai Aliyu Sabi Abdullahi y ace an gwada a baya kuma matakin ya haifar da da mai ido karkashin sabuwar dokar, a cewar sa ba wai tilas ba ne kowace jiha sai ta kafa rundunar ‘yansanda.

en_USEnglish
en_USEnglish