MAJALISAR ZARTARWA TA JIHAR KANO TA AMINCE D DA BAKWAI

Majalisar zartarwa ta Jihar Kano ta amince a fitar da fiye da naira miliyan 27 domin sayen sababbin kwanukan awon da za’a rarraba a kasuwannin daban daban na fadin jahar nan.
Kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya sanar da haka yayin jawabi ga manema labarai game da sakamakon zaman zaman majalisar na wannan mako.
Yace matakin na daga tsarin gwamnati na kaddamar sabon mudun awo a fadin jihar.
Kwamishinan labarun na Kano yace majalisar ta amince a fitar sama da naira miliyan 452 domin gudanar da ayyukan lafiya da lamuran mahalli.
Yace daga cikin kudaden aikin kara da cewa, aikin zaizayar kasa a garuruwan zangon marikita a karamar hukumar Ungogo da Garo a karamar hukumar Kabo zai lankwame fiye da naira miliyan 253
Comrade Mohammed Garba ya yi bayanin cewa, majalisar zartarwar ta Kano ta sahhale a fitar da sama da naira miliyan 84 da nufin sabunta babbar cibiyar lafiya ta karamar hukumar Rimin Gado tare da samar da kayayyakin aiki.
Kwamishinan yace za’a gudanar da makamancin wannan aiki a cibiyar lafiya ta unguwar Dorayi Gabas dake karamar hukumar Gwale.
Haka kuma yace, majalisar ta amince da amfani da naira miliyan 21 domin sayan litattafan darrusan ilimin harkokin Isalama da za’a raba a kananan makarantun sakandare domin amfanin ‘yan aji 1 zuwa uku.
MIK

en_USEnglish
en_USEnglish