WASU ‘YAN KASUWA A AMURKA SUN GANA DA JAMI’AN NAJERIYA GAME DA BATUN SAKA JARI A KASAR NAN

Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi osinbajo ya kammala ziyarar kwadaitawa ‘yan kasuwar Amurka musamman masu masana’antun fasaha kan zuba jari a kasar nan.
Shugabn hukumar bunkasa fasahar zamani Dakta Isah Ali Fantami, ya ce kasar Amurka ta ware Dala miliyan dubu daya domin zuba jari a fannin fasaha, a don haka ne suka kai ziyara kasar ta Amurka tare da ganawa da ‘yan kasuwa da masu manyan kamfanonin fasaha.
Dakta Fantami ya bayyana cewa akalla ‘yan kasuwa da masu kamfanonin fasaha 30 ne suka halarci ganawar.
Ya kuma kara da cewar sunyi anfani da damar suka kuma ziyarci manyan kanfanonin fasaha irin su Google da takwarorin su a fannin na fasaha, wadanda ake saran zasu zuba jari, hakanan kuma ana saran zasu horas da matasan kasar nan akalla dubu ashirin a fannin fasaha.

en_USEnglish
en_USEnglish