AN ZARGI MINISTAN WASANNI DA CINNA WUTAR RIKICIN HUKUMAR KWALLON KAFA TA KASA

Wani dan majalisa mai wakiltar Warri a majalisar dokoki ta tarayya, Mista Daiel Reyenieju ya zargi ministan wasanni, Solomon Dalung, da haifar da rikice-rikice a hukumar kwallon kafa ta kasa bias wasu dalilai na kashin kansa.

Mista Daniel, mai wakiltar Warri ta jihar Delta, ya firta hakan ne yayin da yake jawabin sag a wata kungiyar siyasa ta matasa, inda yace tin da ministan ya kama bakin aikin sa, yake amfani da wasu hanyoyi domin rusa shugabancin hukumar kwallon kafa ta kasa karkashin jagorancin Amaju Pinnick.

Ya kuma ce da sanin hukumar kwallon kafa ta duniya da kuma hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika suka sanya ido a zaben da aka yiwa Amaju Pinnick a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa a shekarar 2014.

Ya kara da cewa, duk da kotun wasanni ta duniya dake kasar Switzerland, ta amince da Amaju Pannick a matsayin shugaban hukumar, amma ministan wasannin yake neman kakaba wanda yake so a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa.

Haka zalika, mista Daniel, ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewa da ya jawa ministan wasanni kunne bias gargadin da shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino ya yi kan cewa za’a dakatar da Najeriya a harkokin wasanni har inda minister Dalung bai mayar da hankali ba a kai.

en_USEnglish
en_USEnglish