RUNDUNAR TSARO TA FARIN KAYA TA TURA JAMI’ANTA 1,200 ZUWA WASU SASSAN JIHAR BORNO DA AKA KUBUTAR DAGA HANNUN BOKO HARAM

Rahotanni daga jihar Borno na cewa rundunar tsaro ta farin kaya wato civil depence ta tura jami’anta 1,200 zuwa wasu sassan jihar da aka kubutar daga hannun mayakan Boko haram.
Babban kwamandan rundunar Muhammadu Gana ne yabayya na hakan, inda ya ce wannan wani shirine na karawa fararen hula kwarin gwiwar sake gudanar da harkokin su na yau da kullum cikin kwanciyar hankali.
Al’umma da dama ne dai a jihar ta Borno sukayi maraba da wannan mataki, inda suka ce yanzu sun san cewa gwamnati ta damu da zaman lafiyar su, inda da yawa daga cikin mazauna yankin suka koma gidajen su.
Jihar Borno dai ta kasance daya daga cikin jihohi da ke fama da rikicin Boko haram, inda al’umma da dama suka rasa rayukan su da dukiyoyi, yayin da har wasu daga cikin yankunan na jihar Borno suka koma karkashin kungiyar ta Boko haram, amma jami’an tsaron kasar nan suka samu nasarar karbo su.

en_USEnglish
en_USEnglish