SAMA DA MUTANE DUBU BIYU NE SUKA RASA MATSUNANSU SAKAMAKON AMBALIYAR RUWA

Hukumomi a kasar nan sun ce sama da mutane 2000 ne zuwa yanzu aka tantance wanda suka rasa matsugunnansu, bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ya faru a garin jibiya dake jihar katsina.
Ambaliyar ruwan wanda tayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da mutum 40.tare da daruruwan gidaje da suka lalace,sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka wayi gari anayi.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, alh aminu waziri ya bayyana cewa gidaje sama da 200 ne suka rushe, wanda tuni kuma aka kwashe mutanan da suka rasa matsugunnin zuwa makarantar firamare dake garin jibya zuwa na dan wani lokaci.
Alh waziri yace akwai mutane da dama da ruwa ya jasu zuwa wasu garuruwa na jamhuriyyar niger,amman an tura da mota domin kwaso gawawwakin mutanen.
Ya kara da cewa ko a watan daya gabata, an sami ambaliyar ruwa a wasu kananan hukumomi na jihar , wanda suka hada da katsina da chiranci da kuma musawa,lamarin da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyin al`umma.
Ana dai samin irin wannan matsala ta rushewar gidaje da kuma asarar rayuka a wasu sassa na kasar nan, sakamakon ruwan saman da a wani lokaci yake sauka kamar da bakin kwarya.

en_USEnglish
en_USEnglish