SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YAYI ALKAWARIN YIN DUK MAI YUWUWA DOMIN GUDANAR DA ZABUKAN BADI CIKIN KWANCIYAR HANKALI DA LUMANA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin yin duk mai yuwuwa domin ganin an gudanar da zabukan badi cikin kwanciyar hankali da lumana.

Shugaban ya ce za’a hada hannu da sukkanin masu ruwa da tsaki domin kaucewa tarzomar data dabai-baye babban zaben shekara ta 2011, lamarin daya sanya tilas har kotun duniya ICC dake hukunta masu manyan laifuka ta gudanar da bincike.

Shugaba Buhari na wadannan kalamai ne a birnin Hague a yayin taron tunawa da kafa shalkwatar kotun ta ICC karo na 20.

Rahotanni sunce, ‘yan najeriya da dama sun rasa rayukan su biyo bayan tarzomar zaben shekara ta 2011 .

Amma shugaba Buhari bada tabbacin cewa, hakan ba zata sake afkuwa a karkashin kulawar gwamnatin sa.

en_USEnglish
en_USEnglish