HUKUMAR NAFDAC TACE NAN BADA JIMAWA BA ZATA FARA GUDANAR DA BINCIKE GA MASU SIYAR DA KAYAYYAKIN ITATUWA

Hukumar kula da ingancin kayayyakin abinci da magunguna NAFDAC ta ce nan bada jimawa ba, za ta fara gudanar da bincike ga masu siyar da kayayyakin itatuwa da ake kunshe su a cikin kasuwanni dake fadin kasar nan.
Shugabar hukumar Farfesa Moji Adeyeye ce, ta bayyana hakan yayin gudanar da wani jawabi a jiya Talata a birnin tarayyar Abuja jiya.
Ta ce, hukumar ta yanke wannan shawarar ne bisa yadda wasu ‘yan kasuwa ke amfani da wasu sinadari mai illatarwa na Calcium carbide a cikin irin kayayyakin itatuwan da suke sarrafawa kafin su kunshe su.
Ta kuma ce hukumar ta NAFDAC ta kula da cewar, nau’ikan ‘ya’yan itatuwar da ake siyarwa ga al’umma na dauke da sinadarin calcium carbide, wanda ya zama wajibi hukumar ta dauki mataki a kai wajan kulawa da ingancin lafiyar al’umma.
Ta kara da cewar, ‘ya’yan itatauwa na kare wasu kwayar cututtuka masu yaduwa a jikin bil adama amma wasu ‘yan kasuwar na kara sinadarin calcium carbide a cikin laimukan nasu.

en_USEnglish
en_USEnglish