RUNDUNAR SOJIN RUWA TA KAMA WASU MUTANE BIYAR DA SUKAI SAFARAR SHINKAFA YAR KASAR WAJE

Rundunar sojin ruwa ta kasa dake gudanar da aikin ta a jihar Akwa Ibom ta kama wasu mutane biyar da yin safarar shinkafa ‘yar waje sama da 828 wacce aka shigo da ita cikin kasar nan.
Kwamandan dake kula da sintiri a yankin Ibaka dake yankin karamar hukumar Mbo, Kaftin Yusuf Idris ne ya bayyana hakan a jiya Talata, inda y ace sun sami nasara kama shinkafar ne da mutanen a wasu mototci kirar kanta yayin da ake loda masu a gabar taku.
Ya kuma ce ko a satin da ya gabata sun sami nasarar kama buhun shinkafa 444 da aka shigo dasu cikin kasar nan.
Kaftin Idris, ya kara da cewar, abun takaicin shine duk da irin tsaro da ake a kan tekun kasar nan tare da hana shigo da shinkafar ‘yar waje, amma har yanzu wasu ‘yan simogal na yin watsi da wannan doka, inda yace jami’an tsaron ba za su gajiya da farautar masu irin wannan halin dabi’ar ba.
Haka zalika ya ce zasu kuma mika mutanen da suka kama zuwa hannu hukumar hana fasa kauri ta kasa kwastan domin gudanar da bincike.

en_USEnglish
en_USEnglish