SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YA AIKAWA MAJALISA WANI KWARYA-KWARYAN KASAFIN KUDI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa da Majalisar Dokokin kasar nan wani kwarya-kwaryar kasafin kudi wanda a ciki ake kyautata zaton samun kudaden zaben shekarar 2019.
Kwarya-kwaryar kasafin kudin na Naira biliyan 242.4 wanda a ciki za a ware kudaden da za a yi zabe a watan Fabrairun shekarar 2019 da su.
Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Bukola Saraki ya bada bayanin kasafin cewa, Hukumar Zabe, za a ware ma ta Naira biliyan 189 sai Ofishin mai bada shawara ga shugaban kasa kan lamuran tsaro, Naira biliyan 4.2 yayin da Hukumar tsaro ta farar hula DSS Naira biliyan 12.2.
Ita kuwa Rundunar tsaro ta Civil Defense, a cikin kasafin za ta samu Naira biliyan 3.5,Rundunar ‘yan sanda kuwa Naira biliyan 30.5.
Haka zalika, Sanata Kabiru Gaya ya ce, kasafin kudin zai tabo ayyuka irin su aikin wutar lantarki na Mambila, sama da shekara 30 ana tunanin aikin wutar a Mambila da ke jihar Taraba, wanda ake saran samar da megawats 3,050
Shugaba Buhari na kokarin zartar da wannan aikin a Mambilla wanda aka yi tunaninsa shekaru sama da 30 da suka wuce, amma ya gagara.
Sanata Gaya, ya bayyana cewa za su yi kokarin bada hadin kansu don ganin an cimma wannan buri.

en_USEnglish
en_USEnglish