MAJALISAR ISRAILA TA AMINCE DA WATA DOKA DA TA BAYYANA YANKIN KASAR A MATSAYIN KASAR YAHUDAWA ZALLA, SABANIN KUDURORIN MAJALISAR DINKIN DUNIYA

Majalisar Israila ta amince da wata doka mai sarkakiya wadda ta bayyana yankin kasar a matsayin kasar Yahudawa zalla, sabanin kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.
‘Yan majalisun Israila 62 ne suka amince da wannan sabuwar doka mai sarkakiya, yayin da 55 suka kada kuri’ar kin amincewa da ita.
A karkashin wannan sabuwar doka, kasar ta Israila zata janye harshen larabci a matsayin harshen hukuma da kuma mayar da gina gidajen Yahudawa Yan kama wuri zauna a matsayin bukatar kasa.
Sabuwar dokar ta kuma bayyana Birnin Kudus a matsayin Babban Birnin Israila, sabanin yadda kasashen duniya ke bukatar ganin sun raba tare da Falasdinawa.
Yan Majalisu Larabawa dake Majalisar sun yi Allah wadai da matakin, yayin da Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana shi a matsayin kwakwaran mataki.
Wannan mataki zai ci karo da duk wani yunkuri na kasashen duniya da kuma Majalisar Dinkin Duniya na sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya.

en_USEnglish
en_USEnglish