MATAIMAKIN SHUGABAN KASA DA WASU GWAMNONIN YAU SUN SHIGA WATA GANAWA TA ZAUREN TATTALIN ARZIKIN KASA

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo da wasu gwamnoni sun shiga wata ganawa ta zauren tattalin arzikin kasa a yau.
Ganawar da rahotanni suka nuna cewa ana yinta ne a fadar shugaban kasa, ta fara ne da karfe sha daya na safe wacce kuma cikin wadanda suka samu halarta akwai gwamnan jihar Katsina da na Sokoto da na Ogun da na Kebbi sai kuma wasu mataimakan gwamna na wasu jihohin.
Taron kamar yadda ya saba gudana a baya ana sa ran zai mayar da kai ne kan al’amuran tattalin arzikin kasar nan.
Har ila yau wasu daga cikin shugabannin manyan ma’akatun gwamnati sun harta wadanda suka hada da Gwamnan babban bankin kasar nan Godwin Emefele da shugaban kampanin mai na kasa NNPC Mai Kanti Baro da sauransu.
Ana sa ran bayan kammala taron zauren tatalin arzikin na kasa zai shaidawa manema labarai batutuwan da aka tattauna domin fahimtar da yan kasa matsayar da aka cimma.
A ranar Laraba ne dai kungiyar gwamnonin kasar nan suka yi wata ganawa ta musamman akan kwamitin asusun gwamnatin tarayya kan Karin mafi kankantar albashi da sauransu wasu batutuwa.

en_USEnglish
en_USEnglish