SHUGABAN AMURKA DONALD TRUMP YA AMINCE DA CEWA RASHA TA YI KOKARIN YIN KATSALANDAN A ZABEN AMURKA NA 2016

Shugaban Amurka Donald Trump ya amince cewa Rasha ta yi kokarin yin katsalandan a zaben Amurka na 2016, zaben da ya ba shi damar zama shugaban kasa. Sai dai yayin wani taron koli da ya yi da takwaransa na Rasha Vladmir Putin ranar Litinin, Mista Trump ya fadi akasin haka.
Wannan furuci na shugaba Trump ya janyo damuwa daga ‘yan majalisar kasar, ciki har da masu goyon bayansa.
Shugaba Trump na karkashin tsaninin matsi domin ya bayyana kalaman da yayi da suka daure kawunan shugabannin duniya, kuma suka fusata ‘yan jam’iyyrsa ta Republican.
Rahotanni dai sun nuna cewa shugaba Trump na son kulla dangataka mai kyau da Rasha.
A yayin da yake ganawa da shugaban Rasha Vladmir Putin ranar Litinin, Trump ya kasa tankawa game da batun kutsen da ake tuhumar Rashar da yi ma tsarin zaben Amurka na 2016.
A madadin haka, sai ya goyi bayan sukar da Mista Putin din yayi cewa tuhumar da hukumomin tsaron kasar ke yi ma Rashar abin dubawa ne.
Mista Trump yayi kokarin kare kansa daga zargin cewa yana tsoron Mista Putin ne, inda ya ce tuntuben harshe ne ya sa ba a fahimce shi ba.
Ya kuma ce gwamnatinsa na daukar abin da ya kira ‘kwakkwaran mataki’ domin kare muradun Amurka da tsarin zabukanta daga duk wata barazana, amma da alama ‘yan jam’iyyarsa ba su gamsu ba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Mitch McConnell ya fito fili ya gargadi Rasha da kada ta kuskura ta sake gwada kutsen da ta yi a 2016.

en_USEnglish
en_USEnglish