HUKUMAR ZABE TA KASAR ZIMBABWE TACE DUKKANIN KURI’UN DA ZA’A KADA ZASUYI TASIRI A BABBAN ZABEN KASAR DA ZA’AYI

A jiya litinin hukumar zabe ta kasar Zimbabwe, tace duk kuri’ar da aka jefa a babban zaben kasar da za’ayiranar 30 ga watan nan zatayi tasiri, kuma za’akare sirrin kuri’a.
Mukaddashin shugabanhukumar zaben kasar Emmanuel Magade ne ya bayyana hakan ga manema labarai, da jakadu, da ‘yan saido a jiya Litinin, da zummar karfafa gwiwa akanzaben da za a gudanar.
Yace “Tabbacin da zai baiwa jama’a da suka taru shine babu wata kumbiya-kumbiya wajen tabbatar da kowa zaijefa kuri’arsa cikin sirri.
Wannan tabbacin yana zuwa ne a daidai lokacin da babbar jam’iyyar hamayya MDC tace zata fara zanga-zanga daga yau Talata, idan hukumar tagaza bin yin bukatun da suka gabatar mata da suka hada da tabbatar da cewa ba’ayi magudi a zabenba.
Jam’iyyar tana zargin hukumar zaben da laifin shirin yin magudi a madadin jam’iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar a yanzu, kamar yadda tayi zamanin nmulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.

en_USEnglish
en_USEnglish