JIMLAR SANATOCI 15 SUNYI SAUYIN SHEKA DAGA JAM’IYYAR APC ZUWA PDP

yan jam’iyyar APC a majalisar wakila 32 ne sukayi kaura zuwa jam’iyyar PDP.
A zaman majalisar na talatar nan, karkashin jagorancin shugaban majalisar Yakubu Dogara wasu Karin ‘yan majalisar guda hudu ‘yayan jam’iyyar ta APC daga jihar Oyo sunyi sauyin sheka zuwa jam’iyyar ADC.
Hakan ya nuna jimlar mambobin majalisar wakilai ‘yan jam’iyyar APC guda 36 ne sukayi kaura daga jam’iyyar.
Shugaban majalisar Yakubu Dogara shine ya karanta wasikar da masu sauyin shekar suka rubuta domin sanar da shugabancin majalisar matakin su.
Sai dai sabanin yadda lamarin yake a majalisar dattawa, jam’iyyar APC na ci gaba da rike kambunta na rinjaye a zauren majalisar ta wakilai.
Bayan ficewar Sanatoci guda 15 daga APC, yanzu jam’iyyar PDP ce keda rinjaye a zauren majalisar mai wakilai 109.

en_USEnglish
en_USEnglish