WANI LAUYA YA SOKI DOKAR TSARIN BAIWA MATASA DAMAR TSAYAWA TAKARA

Wani lauya mai zaman kansa anan Kano, Barrister Abdulkareem kabir Maude Minjibir yace tsarin dokar baiwa matasa damar tsayawa takara da shugaban kasa ya sanyawa hannu ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan.
Barrister maude minjibir ya bayyana hakan ne a talatar nan ta cikin shirin sharia aikace na nan gidan radion Dala.
Barrister Minjibir ya kara da cewa kundin tsarin mulkin kasa ya tanadi irin mutanan da yakamata su tsaya takarar sanata ko dan majalisa da dai sauran mukamai.
A zaman na yau dai an tattauna batutuwa da dama da suka shafi sharia.

en_USEnglish
en_USEnglish