GWAMNATIN SUDAN TA SANYA HANNU KAN YARJEJENIYAR SHARE FAGE TSAKINTA DA KUNGIYAR YAN TAWAYEN KASAR

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta sa hannu kan wata yarjejeniyar share fage tsakanin ta da wata babbar kungiyar ‘yan tawayen kasar domin raba iko, da zummar kawo karshen yakin basasar kasar na kusan shekaru biyar.
Sai dai kuma wata gamayyar jam’iyyun hamayya 9 sun ki saka hannu a wannan yarjejeniyar inda suka ce sun dauki matakin ne saboda ba a karbi shawarwarin da suka bayar ba.
Yarjejeniyar dai ta nuna cewa har yanzu shugaba Salva Kir zai ci gaba da zama shugaban kasar, yayin da shugaban ‘yan tawaye Riek Machar, zai ci gaba da rike tsohon mukaminsa na mataimakin shugaban kasa na farko.
Haka kuma yarjejeniyar ta bukaci a samar da majalisar dokoki mai mutane dari biyar da hamsin a shirin mika mulki, sannan a samar da wasu mataimakan shugaban kasa mutane 4 kuma daya daga cikin su za ta kasance mace.
Kungiyar yankin kasashen Afirka ta Gabas ce da ake kira IGAD ta shiga tsakani akan wannan yarjejeniyar domin samar da daidaito.

en_USEnglish
en_USEnglish