MATAIMAKIN JAKADAN AMURKA YA NUNA RSHIN JIN DADINSA KAN TABARBAREWAR TSARO A NAJERIYA

Mataimakin Jakadan Amurka a Najeriya David Young yanuna rashin jin dadinsa kan yadda halin tsaro ke kara tabarbarewa a Nigeria wanda yake sanadiyyar asarar rayuka.
Jakadan ya yi wannan maganr ce a lokacin da ya zagaya jihohin Zamfara da Kaduna, inda ya ce tashe-tashen hankula bai tsallake kowa ba- da makiyaya, da manoma, da kabilu mabanbanta, da musulmi da kirista dukkaninsu wannan rikici ya rutsa da su.
Ya ce ya fahimci cewa lallai wannan lamari ne mai rikitarwa kuma babu maslaha kai tsaye cikin sauki amma hanyar da suke ganin za ta iya zama mafita ita ce hada karfi da karfe domin murkushe dukkan mutanen da ke tayar da fitinu ta yadda duk wanda aka kama da laifi doka za ta yi aiki akansa.
Jakadan ya ce suna sane cewa gwamnati na kokari matuka amma saboda irin asarar rayukan da ake samu akwai bukatar gwamnati ta kara kwazo.
Young, ya bayar da shawara cewa akwai bukatar kirkiro ayyuka na ci gaba domin samarwa matasa aikin yi kuma a cewarsa, sanin muhimmancin wannan ne yasa Amurka ta hada gwiwa da Najeriya wajen inganta fannonin ilimi, da lafiya, da tattalin arziki da noma da sauran bangarori da zummar samar da aikin yi ga matasan kasar domin kyautata makomarsu don gujewa zama bata-gari.

en_USEnglish
en_USEnglish