MINISTAN SHARI’A YA SHAIDAWA RUNDUNAR TSARO TA YAN SANDA CEWA BATADA HUJJA DANGANE DA ZARGIN DA TAKEWA SHUGABAN MAJALISAR DATTAWA

Ministan shari’a kuma atoni JanarAbubakar Malami ya shaidawa rundunar tsaro ta ‘yan sanda cewa bata da hujja dangane da zargin da takewa shugaban majalisar dattawa sanata Bukola Saraki da gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmad kan harin da aka kai bankin Offa wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 31 a jihar Kwara a watan Aprilu.
A wata wasika da ministan ya rubuta ranar 22 ga watan Yuni ya shawarci babban sifetan ‘yan sanda Ibrahim K Idris cewa ya hanzarta bincike kan batun tare da bibiyar al’amuran da suke da sarkakiya cikin zargin, kafin ayyana sanatan Sarki a matsayin mai hannu dumu dumu a fashin da aka yi.
Yusuf Abdulwahab wanda shi ne shugaban ma’aikata na gwamna Abdulfatah Ahmad, na jihar Kwara,na daga cikin wadanda rundunar ‘yan sanda ta kama bisa zargin hadin kai da wadanda ake zargi sun yi fashi a bankin sai dai kotu ta wanke shi inda ta ce babu wata hujja data ke nuna da hannunsa a cikin fashin da aka yi.
Ministan ya cemutun shida ne kawai za su gurfana gaban kotu bisa zargin fashida makami da kuma kisa sai kuma wani mutun Olalekan Alabi wanda mataimaki na musamman ne ga gwamna Abdulfatah zai fuskanci tuhuma bisa mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
A ranar litinin din data gabata ne Sanata Bukola saraki ya bayyana cewa babu bukatar ya amsa gayyatar da rundunar tsaron yan sanda tayi masa bisa dogaro da wasikar ministan shari’ar wacce ta nuna babu wata hujja da ta nuna yana da hannu cikin zargin da ake masa.

en_USEnglish
en_USEnglish