RUNDUNAR SOJIN SAMA TA KASAR NAN ZASU FARA GUDANAR DA KAI HARI TA SAMA AKAN YAN TA’ADDA

Tun Bayan umarnin da Shugaban kasa muhammadu Buhari ya bai wa rundunar sojin saman kasar nan na ta kai manyan jirage zuwa jihar Zamfara domin dakatar da kashe-kashen da ake yi a jihar.
Wannan gagarumin farmakin da sojojin saman kasar nan za su fara kaddamarwa da manyan jiragen yaki,mai suna ‘Operation Dirar Mikiya
Wannan wani farmaki ne ta sama domin fatattakar ‘yan bindiga daga Jihar Zamfara da kuma yankunan ta.
Babban kwamandan rundunar sojin kundunbala na mayakan saman, Air Vice Marshall Akpasa Samson Okon, wanda shi da kansa ke jagorantar wannan farmaki.
Ya bayyana cewa rundunar ba ta da inda manyan jiragen yaki za su rika sauka ko tashi daga Gusau. Yanzu ana amfani da filin jirgin saman Katsina a cewarsa, don haka ne aka jibge jirage masu yawa a can, sannan wasu da yawa na nan tafe har da kuma dakaru na musamman su ma na bisa hanya da kayan aiki.
Ya kara da cewa wannan wani mataki ne na a-yi-ta-ta-kare, da suke son kaddamarwa. A don haka ne rundunar ta kawo kayayyakin yaki da suka hada da manya-manyan jiragen yakin sama.

en_USEnglish
en_USEnglish