RUNDUNAR TSARO TA CIVIL DEFENCE ZATA HORAS DA JAMI’AI SAMA DA DUBU ASHIRIN

Rundunar tsaro ta Civil Defence ta ce ta horas da jami’an ta sama da dubu ashirin kan yadda za’a tsaurara matakan tsaro a fadin kasar nan, ta hanyar amfani da kayan aiki na zamani.
Kakakin rundunar na kasa Emmanuel Okeh, ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai jiya a birnin tarayya a Abuja.
Yace dukkanin jami’ain da aka horas an zabo su ne a dukkanin ofisoshin hukumar da ke sassa daba-daban a fadin kasar nan.
Emmanuel Okeh ya kara da cewa horon na zuwa ne biyo bayan umarnin da rundunar ta samu daga ma’aikatar lura da harkokin cikin gida, domin kara inganta matakan tsaro a kasar nan.
Kakakin rundunar ta civil defence yace an dauki matakin horas da jami’an ne domin shirin ko ta kwana, inda yace za’a cigaba da bawa dukkanin jami’an rundunar horo kan yadda zasu yi amfani da makaman aiki, domin ta hakan ne za’a inganta tsaro a kasar nan.

en_USEnglish
en_USEnglish