RUNDUNAR YAN SANDAN JIHAR ZAMFARA TA TABBATAR DA JAN DAGA DA WASU YAN FASHI

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Zamfara ta tabbatar da jan daga tsakaninta da wasu gungun ‘yan fashi a kasuwar shanu da ke Talatar Mafara da ke Jihar Zamfara, inda suka samu nasarar kubutar da wasu mutane tara da sukai kokarin sacewa.
kakakin hukumar ‘yansandan Jihar Muhammad Shehu ne ya tabbatar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai a garin ajiya talata.
Muhammad Shehu ya ce, da misalin karfe 4 na yamma ne wasu ‘yan fashi suka dira kasuwar shanu a Talatar mafara, inda suka yi kokarin satar shanu da kuma wasu mutane tara, wanda a yanzu hukumar ‘yansanda ta sami nasarar kwato su.
Muhammad ya kuma ce, a yanzu haka sun kama mutane 12 da ake zargi da yin fashin, wanda kuma da zarar sun kammala bincike zasu gurfanar da su gaban kuliya.
Ya kara da cewa ya nemi mutanen garin, da su kasance masu saka ido a yankunan su, tare da sanar da hukumar ‘yansanda abin da ke faruwa.

en_USEnglish
en_USEnglish