WATA KOTU TA WANKE TSOHON GWAMNAN JIHAR SOKOTO

Wata babbar kotu dake jihar Sakkwato ta wanke tsohon Gwamnan jihar Attahiru Bafarawa daga tuhumar karkatar da kudi da sauransu.
Mai shari’a Bello Abbas ya wanke dan tsohon gwamnan ne tare da wadansu mutane hudu daga dukkan tuhume-tuhume da Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) take musu.
Alkalin kotun ya ce mai gabatar da kara bai nuna kwararan shaidu da suke tabbatar da tuhume-tuhumen da ake musu ba.
Ya kara da cewa Babu kwararan hujjoji da za su tabbatar da cewa mutanen sun aikata laifukan da ake zargin su dashi.
Sai dai hukumar EFCC ta ce ba ta gamsu da hukuncin ba, kuma za ta daukaka kara, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

en_USEnglish
en_USEnglish