MUTANE BIYU NE SUKA RASA RAYUKANSU A ZABEN KASAR ZIMBABWE

Comments are closed

A kalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu a Harare babban birnin Zimbabwe a jiya Laraba,a lokacin da jami’an tsaro suka yi arangama da masu zanga-zanga wadanda ke bukatar a gaggauta bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar.
Biyo bayan zanga zangar ne rundunar ‘yan sandar kasar ta bukaci gudun mowar soja da su taimaka domin a samar da zaman lafiya a Harare fadar gwamnatin kasar.
Yayin da ‘yan kasar ke jiran sakamakon zaben shugaban kasar tun ranar littinin din da ta gabata, wanda shine iri na farko a cikin shekaru 38 da aka gudanar ba tare da sunan tsohon shugaban kasar Robert Mugaba a takadar jefa kuri’a ba.
Jinkirin da aka samu ne na kin bayyana sakanamkon zaben yasa ‘yan adawa cewa shugaban su Nelson Chamisa ne ya yi galaba akan shugaba Emerson Mnangagwa.
Tsohon Prime Ministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn shine ya jagoranci tawagar kungiyar tarayyar Amfrica domin sa ido a zaben.
Shugaba Mnangagwa wanda jamiyyarsa ta ZANU -PF ke kan gaba a sakamakon da aka riga aka fidda ya bukaci jama’ar kasar su zauna lafiya.

Comments are closed.