MATAIMAKIN GWAMNAR JIHAR KANO YA MUSANTA JITA JITAR DA KE YAWO A GARI CEWA YA BAR JAM’IYYAR APC ZUWA JAM’IYYAR PDP

Comments are closed

Mataimakin gwamnan jihar kano farfesa Hafizu Abubakar ya musanta jita jitar da ke yawo a gari cewa ya bar jam’iyyarsa ta APC zuwa jam’iyyar PDP a jiya.
Da yake ganawa da manema labarai Farfesa Hafizu ya ce bai fita daga jam’iyyar APC ba kuma har yanzu shi ne mataimakin gwamnan jihar kano.
Ya kuma ce bai ajiye aiki ba kamar yadda wasu ke yadawa a kafafen sadarwa na internet, hasali ma yanzu yana babban birnin tarayya Abuja inda ya kai ziyarar aiki ga zauran majalisar Ilimi na kasa.
Rahotan fitar mataimakin gwamnan daga APC ya yi karfi ne bayan da jam’iyyar PDP a jiya ta ce tana maraba da mataimakin gwamnan da gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal zuwa jam’iyyar a shafinta na twitter.
Farfesan ya ce dangane da makomar siyasarsa, sai lokacin da ya dace ya zo sannan zai bayyanawa duniya matsayarsa bayan yayin tuntuba da shawarwari.
Sai dai ya zargi wasu jam’ian gwamnati da yada wannan jita jita mara tushe.
A ranar 30 ga watan Yuli ne Farfesa Hafizu Abubakar ya rubuta takardar korafi ga rundunar yan sanda da rundunar tsaro ta farin kaya yana shaida musu cewa rayuwarsa na cikin hadari sannan gwanatin kano na shirin biyan wasu matasa su yi zanga zangar nuna kin goyon bayansa a gwamnatin.
Mataimakin gwamnan dai ba ya shiri da gwamna Ganduje kasancewar gwamnan shi ma baya ga miciji da tsohon gwana sanata Rabiu Musa kwankwaso wanda mai gidan mataimakin gwamnan ne a siyasa.

MIY

Comments are closed.