WANI BINCIKE YA BAYYANA CEWA YAWAN AMFANI DA ROBA DA GILASHI NA KARA JAWO DUMAMAR YANAYI A FADIN DUNIYA

Comments are closed

Wani bincike da Jami’ar Hawaii ta gudanar ya nuna cewa roba da gilashi na kan gaba wajen haddasa dumamar yanayi a fadin duniya.
Masana ilmin kimiyya masu rubutu a mujallar nan mai suna PLOS ONE sun bayyana hakan ne a jiya Laraba inda suka ce leda na fitar da turiri musamman lokacin da hasken rana ya buge ta.
Masanan sun gudanar da binciken ne ta hanyar gwaji a kullun akan abubuwan dake da nasaba da robar da ake zuba ruwa ciki, ko kuma ledar da ake sa kayayyakin da aka yi sayayya a kantuna ko kuma wadda aka zuba abinci.
Kamar yadda babban jami’in gudanar da bincike David Karl na Jami’ar Hawaii ya ce, roba tana a matsayin abinda keda tasiri ga gilashi wanda ake sa ran yana kara dumamar yanayi.
Iskar gas din nan mai launi iri daban-daban da ledar da ake sarrafawa sune kan gaba wajen samar da canjin yanayi.

Comments are closed.