GWAMNAN JIHAR NAIJA YACE BABU WANI DALILI DA ZAI SANYA SHI BARIN JAM’IYYAR APC

Comments are closed

Gwamnan jihar Naija Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi watsi da rahotan dake cewa, yana shirye-shiryen sauya sheka daga APC zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
A zantawa da Muryar Amurka a Minna, ya ce zancen bashi da tushe balle makama, yana mai cewa, babu wani dalili da zai sanya shi barin jam’iyyar APC.
Gwamnan Abubakar yace yana cikin gwamnonin da suka dinga zagayawa suna yiwa ‘yan uwansu nasiha su ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar.
Ya yi bayanin cewa, dukkan wadanda suka canja sheka basu fita don wata akida ba, inda yace gudun bincike da kuma neman mukami ya sanya wasu ke sauya sheka.

Comments are closed.